Talata 1 Satumba 2026 - 20:54
Ilimin Iyali | Daga Farko Har Ƙarshe na Tarbiyyar Yara; Wane Irin Iyali ne Zai Iya Shirya ‘Ya’yansa Domin Duniyar Yau? (1)

Hauza/ Tarbiyyar yara a duniyar yau ta zama ɗaya daga cikin manyan damuwar iyaye; amma shin ya kamata iyaye su tsara yaro bisa abin da suke so, ko kuma su samar masa da yanayin da zai ba shi damar bunƙasa yadda Allah Ya halicce shi? Hujjatul Islam Reza Yusufzadeh, masani kuma mai ba da shawara kan iyali da aure, ya yi bayani kan buƙatar sauya fahimtar tarbiyyar yara.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | A zamanin da yaro yake fuskantar nau’o’in tunani da halaye daban-daban daga gida, makaranta, kafafen yaɗa labarai da duniyar intanet, tarbiyya ba ta takaita ga umarni da sarrafa ɗabi’a kawai ba. Tambayar ita ce: Ta yaya iyali zai tarbiyyantar da yaro mai ’yancin tunani, mai tushe, kuma mai juriya?

Wannan rahoto ya samo asali ne daga kashi na farko da na biyu na wani taron bita na musamman kan “Tarbiyyar yara da salon sadarwa tsakanin ma’aurata”, wanda Hujjatul Islam wal Muslimin Reza Yusufzadeh, masani kuma mai ba da shawara kan iyali da aure, ya gabatar.

Tarbiyya: Sassaka mutum-mutumi ne ko aikin lambu?

A cewar Hujjatul Islam Yusufzadeh, akwai manyan dabaru guda biyu wajen tarbiyyar yara. Na farko shi ne tsarin sassaka mutum-mutumi ko ƙera abu, inda ake ɗaukar yaro a matsayin halitta marar tasiri, sannan iyaye su yi ƙoƙarin canza shi kai tsaye ta hanyar magana, nasiha, umarni, lada da hukunci.

Wannan hanya na iya samun amfani a wasu ƙananan fannoni, kamar koyar da wani wasa ko wata fasaha, amma idan aka mayar da ita babban tsarin tarbiyya, tana iya haifar da matsaloli ga tsarin tunani da halayyar yaro.

Yara yayin da suke girma, musamman daga lokacin balaga zuwa samartaka, sukan fara nuna juriya ga irin wannan tsarin. Matashi na iya fara ƙin wasu hanyoyin kulawa, nasiha, lada ko takunkumin da iyaye suke amfani da su.

A cewar wannan masani, samartaka wani lokaci ne mai muhimmanci da mutum yake fara neman ’yanci da sake gano halinsa. Amma tsoron iyaye game da makomar yaro kan sa su ci gaba da amfani da tsarin sarrafa shi fiye da kima.

Lokacin da iyaye suke son yaro ya zama abin da suke so

Tsarin sassaka mutum-mutumi yana sa iyaye su fi mayar da hankali kan abin da su suke so yaro ya zama, maimakon abin da yaron yake da shi na dabi’a, baiwa da halaye.

Wani lokaci iyaye kan yi ƙoƙarin cike gibin da suka samu a rayuwarsu ta hanyar ’ya’yansu. Wani uba ko uwa na iya son yaro ya samu abin da su kansu ba su samu a lokacin ƙuruciyarsu ba.

Haka kuma iyaye kan kafa wa yaro wata hanya tun kafin su fahimci abin da yake so ko baiwarsa; kamar tilasta masa ya karanci likitanci ko ya zaɓi wata sana’a, alhali shi yana da sha’awar wani fanni daban.

Wannan salon tarbiyya yana kama da rubuta wani tsari ko algorithm da ake son yaro ya bi ba tare da la’akari da bambancin halayensa ba.

Amma mutane masu hali da tushe ba haka suke ba. Mutane suna da bambance-bambance, kuma mutum mai tushe ba ya sauya halinsa kawai saboda yanayin da yake ciki.

Tsarin lambu: Girmama bambancin yara

A tsarin lambu, iyaye ba sa ƙoƙarin tilasta wa kowace shuka ta zama iri ɗaya. Suna samar da yanayin da ya dace domin kowace shuka ta bunƙasa bisa irin halayenta.

Haka ma yara suke. Yaro ɗaya ba ya zama kamar wani. Ko ’ya’ya daga iyali guda suna iya bambanta sosai.

Wasu yara suna son zama cikin mutane, wasu kuma sun fi natsuwa a gefe guda. Wasu suna da ƙarfin jagoranci, wasu suna da wasu baiwa na daban. Saboda haka, bai kamata a kwatanta yara da juna ba.

Allah Ya halicci mutane da bambance-bambance, kuma haɗuwar dabi’ar da mutum ya zo da ita da kuma muhalli da yake rayuwa a ciki suna taka rawa wajen gina halinsa.

Rudin cewa iyaye za su iya sarrafa komai

A tsarin sassaka mutum-mutumi, iyaye kan shiga cikin rashin fahimtar cewa suna da cikakken iko kan rayuwar yaro. Wannan yana sa su ɗauki nauyin da ya fi ƙarfinsu, har su shiga damuwar zuciya kuma su gaji da tarbiyya.

Ya kamata uba da uwa su tsaya a matsayinsu, su yi abin da ya rataya a wuyansu, ba tare da ƙoƙarin ɗaukar nauyin Allah, ’yan’uwa, dangi, makaranta, al’umma, yanayi da ma yaron kansa ba.

A tsarin sarrafa yaro, ana mai da hankali kan halayen da ake gani: taurin kai, fushi, faɗa da abin da yaro yake yi ko ba ya yi.

Amma a tsarin lambu, tambayar ita ce: Me yake tunani? Me yake ji? Wace buƙata yake da ita? Wace ma’ana yake ba wa abin da yake faruwa?

Tushen mutum ya fi halayen waje muhimmanci

A wasu daga cikin littattafan marigayi Malam Ali Safa'i Ha'iri, an jaddada muhimmancin tushen hali, ’yanci da tunani.

Idan tushen mutum ya yi ƙarfi, zai iya tsayawa da ƙafafunsa ko da yana cikin muhalli mai cike da rikice-rikice.

Saboda haka, a tarbiyya bai kamata a mai da hankali kawai kan halayen da ake gani ba. Ya kamata a fahimci abin da yaro yake fahimta, abin da yake ji, yadda yake ba wa abubuwan da ke faruwa ma’ana, yadda yake zaɓi, abin da yake sha’awa, baiwarsa, abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so.

Haka kuma ƙauna da sha’awar yaro suna da muhimmanci, musamman a ƙuruciya.

A cikin ruwayoyi an jaddada muhimmancin tarbiyyar yara bisa ƙaunar Annabi (S.A.W.A), Ahlulbaiti (A.S) da Alƙur’ani. Samar da wannan ƙauna na buƙatar basira da kirkirar hanyoyin da suka dace da kowane yaro.

Gudun tsawaitawa za mu tsaya a nan, sai mun haɗu a rubutu na biyu inda za mu karkare wannan bahashi in sha Allah.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha